Mutane da yawa
sun san Mabudi a matsayin daya
daga cikin mahimman mukaman fadar
Hadejia Hasali ma dai ana sane da unguwa guda
da ake kira Tudun Mabudi. Sai dai
da yawa ba’a san tarihin da mukamin da yake dashi ba.
Wannan kuwa ya faru ne domin
shi kansa tarihin Hadejia
babu rubutacce sai takaitaccen rubutun
da maigirma Tafidan Hadejia Alhaji Abdu Maigari yayi a kan kafuwar garin da kuma jerin sarakuna da suka yi mulki.
Ma’ana babu bayani kan gidajen sarauta
sai dai ambatansu jifa-jifa.
Saboda haka an dogara ne da abin da magabata da sauran dattawa suka ji ko suka
gani suka fada.
Sarautar Mabudi , tsohuwace a fadar hadejia wacce take
shahara tun lokacin sarakunan Hadejia na da can kafin zuwan turawa, watau lokacin
Usmaniyya. Koda yake ba’a sami hakikanin lokacin da sarautar ta fara ba
amma an samu daidaituwar bayani kan shaharar
Mabudi Abubakar Hausa wanda aka ce yayi zamani da sarkin Hadejia Buhari
zuwa Sarki Umaru sai kuma lokacin da
yafi kasaita wanda yake shine lokacin
Sarki Haru Babba.
A wani kauli an ce lokacin Haru Babba ne ya zama
Mabudi watau a da jarumin fada ne kawai ba mikami.
Zuriyar gidan Mabudi a yau ana danganta ta gas hi Mabudi Abubakar Hausa.
Ita wannan zuriya a yau ana kwatanta ta
da gidaje biyu wajen yawa a Hadejia wato zuriyar gidan Sarkin Arewa da gidan Galadima. Bayan
gidaje a wadansu unguwanni da kauyuka
daukacin unguwar Tudun Mabudi duk
zuriya guda ne.
An samu cewa
Mabudi na da can daga Abubakar Hausa
zuwa Mabudi Zakar Muhammad sun rike
kasashe. Kamar yadda tarihi ya nuna , kafin zuwan turawa wanda sukayi gundumomi wato
jimillar, kasashe da garuruwa a warwatse
suke karkashin Hakiman da suke
zaune a gari tare da Sarki yayin
da wakilan garuruwan suke
biyowata hannun su kan al’amuran garuruwansu.
Daga
cikin garuruwan da suka zama a
karkashin Mabudi sun hada da Kafin Hausa, Gatafa, Guyu, Auyakayi, Garin Gabas, Dakido, Toni
Kutara, da wadansunsu.
Yayin da aka
zo jimilla wanda yazo lokacin Mabudi
Muhammadu zamanin Sarki Abdulkadir sai aka bar Mabudi da Garun Gabas da Toni Kutara sauran garuruwa kwa aka yi
musu hakimai kamar Tafida a Dakido, bangaren Kafin Hausa da farko a
kabaiwa Galadima, daga baya aka rabata bulangu aka baiwa Wambai da masarautar sa shekato,
Sarkin Bai a Kafin Hausa kanta.
Tsarin gudunmomi da aka yi da Mabudi sune kamar
haka:-
Birniwa-(S/Arewa), Kaugama -(Madaki), Dakido
–(Tafida), Garun Gabas – (Mabudi), K/Hausa- (S/Bai), Guri –(Chiroma),
K/kasamma- (S/Dawaki), Auyo-(S/Auyo), Bulangu/Tashen a- (Wambai).
Daga baya har
ila sai aka dawo aka dauke kasa daga
Mabudi wadda ba’a tabbatar da
dalili ba , ya dawo sai zaman
fada watau a Dandalma. Koda yake anci gaba da nada Mabudi kamar yadda ake nada sauran Hakimai amma ya
kasance sai dai harkar fadanci kawai.