Ana ce dashi Muhammadu
Dan Majeri. Ya gaji Mabudi Zakar wanda
yayi mutuwar yaki da turawa a 1906. Koda yake ba zuriyar Mabudi Abubakar bane
amma yana daya daga cikin mukarrabansa. Sarki Haruna Mai Karamba, shi ya nada shi a 1906. Mabudi
Muhammadu shima ya ci gaba da rikon kasashe. Ya samu rikon Garin Gabas A wannan
lokaci an barmasa. Garin Gabas da Toni kutara da wadansunsu. Daga kansa akayi jimilla A wannan
lokacin an barma sa Garin Gabas da Toni kutara a matsayin hakimi amma daga baya aka mai da shi ba kasa, ko da yake ba’a
samu dalilin hakan ba. Tun daga kan Mabudi Muhammadu, Mabudi ya daina rikon
kasa, koda yake an ci gaba da na su kamar sauran Hakimai.
No comments:
Post a Comment