Ya kasance Mabudi na
farko da ya shahara. An kasa tabbatar da
lokacin da ya fara sarauta amma an sami cewa Sarki Buhari shi yi nada shi. Ance
tun Buhari yana dan Sarki ya daukake shi
suka shaku, Saboda haka Jaruntarsa. Tare
da Mabudi abubakar hausa, Buhari yayin da ya zama Sarki yayi yake- yakensa har ALLAH ya karbi ransa bayan yakin Gogaram
a1862. An bada labarin cewa Mabudi Hausa
shi ya kafa Kafin Hausa a matsayin wajen zaman Dako na zamanin yaki. Lokacin
da Sarki Damagaram Tanimu ya kawo mamaye Hadejia Mabudi Hausa, yana
daya daga cikin manya jarumai kamar su
Sarkin Aewa Tatagana, Sarkin Yaki Jaji da sauransu wadanda suke dakon bangarorin
Gari da lura fitar mutane.
Har ila rayuwar Mabudi
Abubakar Hausa, Sarki Haru Babba yayi zamanin sa 1965-85 wadanda ya kara masa daukaka da samun
garuruwa karshinsa. Ance Mabudi Abubkar Hausa yana da dawaki sama da dari
uku da Barade ko kaca kamu, wanda suka hada Sarkin Rafi,
Audun Mabudi, da Ashe wanda aka samo Unguwar ‘A’ ta nan sunan Uguwar ya samu,
Maidugu wanda Kafin Hausa ke kar shinsa
da wadansunsu.
Ance bayan mutuwar Sarki
Haru Babba, Mabudi Hausa da shamakin su suka dora Sarki Muhammadu kan karagar
saurata suka kira sauran
sarakuna suyi mubaya’a, kuma hakan akayi. Mabudi yayi zamani da Sarakunan Hudu
Buhari, Umaru, Haru Babbba. An kiyasta ya rasu 1886-1899 watau zamanin Sarki
Muhammadu.
No comments:
Post a Comment