Thursday, 16 February 2017

TARIHIN SARAUTAR MABUDI A FADAR HADEJIA

Mutane da yawa  sun san Mabudi a matsayin daya  daga cikin  mahimman mukaman fadar Hadejia Hasali ma dai ana sane da unguwa guda  da ake  kira Tudun Mabudi. Sai dai da yawa ba’a  san tarihin  da mukamin da yake dashi ba.
Wannan kuwa ya faru ne  domin  shi  kansa tarihin Hadejia babu  rubutacce sai takaitaccen rubutun da maigirma Tafidan Hadejia Alhaji Abdu Maigari yayi  a kan kafuwar garin  da kuma jerin sarakuna da suka yi mulki. Ma’ana babu  bayani kan gidajen sarauta sai dai ambatansu jifa-jifa.
Saboda haka an dogara ne da abin  da magabata da sauran dattawa suka ji ko suka gani suka fada.
Sarautar Mabudi , tsohuwace  a fadar hadejia wacce  take  shahara tun lokacin sarakunan Hadejia na da can kafin zuwan turawa,  watau lokacin  Usmaniyya.  Koda yake ba’a  sami hakikanin lokacin da sarautar ta fara ba amma an samu daidaituwar bayani kan shaharar  Mabudi Abubakar Hausa wanda aka ce yayi zamani da sarkin Hadejia Buhari zuwa Sarki Umaru sai  kuma lokacin da yafi  kasaita wanda yake shine lokacin Sarki Haru Babba.
A wani kauli an ce lokacin Haru Babba ne ya zama Mabudi watau a da jarumin fada ne kawai ba mikami.
Zuriyar gidan Mabudi a yau  ana danganta ta gas hi Mabudi Abubakar Hausa. Ita wannan zuriya  a yau ana kwatanta ta da gidaje biyu  wajen  yawa a Hadejia wato zuriyar  gidan Sarkin Arewa da gidan Galadima. Bayan gidaje a wadansu  unguwanni da kauyuka daukacin unguwar  Tudun Mabudi  duk  zuriya guda ne.
An samu cewa  Mabudi  na da  can daga Abubakar  Hausa  zuwa  Mabudi Zakar Muhammad  sun rike  kasashe. Kamar  yadda  tarihi ya nuna , kafin  zuwan turawa wanda  sukayi gundumomi  wato  jimillar, kasashe da garuruwa a warwatse  suke karkashin Hakiman da suke  zaune a gari tare da Sarki  yayin da  wakilan garuruwan  suke  biyowata  hannun su  kan al’amuran garuruwansu.
Daga  cikin  garuruwan da suka zama a karkashin  Mabudi  sun hada da Kafin Hausa, Gatafa, Guyu, Auyakayi,  Garin Gabas, Dakido,  Toni  Kutara, da wadansunsu.
Yayin  da aka zo jimilla wanda yazo  lokacin Mabudi Muhammadu  zamanin Sarki Abdulkadir  sai aka bar Mabudi da Garun Gabas  da Toni Kutara sauran garuruwa kwa  aka yi  musu hakimai kamar Tafida a Dakido, bangaren Kafin Hausa da farko a kabaiwa Galadima, daga   baya  aka rabata bulangu aka baiwa  Wambai da masarautar sa  shekato,  Sarkin Bai a Kafin Hausa kanta.
Tsarin gudunmomi da aka yi da Mabudi sune kamar haka:-
Birniwa-(S/Arewa), Kaugama -(Madaki), Dakido –(Tafida), Garun Gabas – (Mabudi), K/Hausa- (S/Bai), Guri –(Chiroma), K/kasamma- (S/Dawaki), Auyo-(S/Auyo), Bulangu/Tashen a- (Wambai).

Daga baya  har ila sai aka dawo aka dauke kasa daga  Mabudi  wadda ba’a tabbatar da dalili ba ,  ya dawo sai  zaman  fada watau a Dandalma. Koda yake anci gaba da nada Mabudi  kamar yadda ake nada sauran Hakimai amma ya kasance sai dai harkar fadanci kawai.

No comments:

Post a Comment