🎫
Mabudi Zakar ya gaji Abubakar Hausa wanda shine
mahaifinsa. Sarki Muhammadu Mai Shahada shine ya nada shi . An Kiyasta a 1899.
Mabudi Zakar gwarzo ne kamar Sarkin da
yayi zamani dashi. Ance bayan runduna da yayi gado ya kara yawan
dawakinsa sama da arbamiya. Ya samu Karin, Garuruwa karkashin sa wanda suka
hada da Gatafa, Auyakayi, Ayan, Guyu, da
wadansunsu.
An samu cewa Mabudi
Zakar na daya daga cikin jarumai bakwai da turawa suka bukaci Sarki Muhammadu ya sadaukar
ko mika kansa ga turawan lokacin suka takali Hadejia da yaki. Sauran
sune Sarkin Arewa Amadu, Sarki Dawaki
Umar Dangazau, Sarkin yaki Muhammadu, Jarma Warkaci, da Shamaki Malami.
Wannan na daga
cikin abinda yaja yaki da turawa inda Sarki Muahammadu tare da dukkan wannan Jarumai aka karsu. wannnan snie dalilan cewa Sarki Muhammdu Maishada. A
gidan Mabudi mai sunan Mabudi Zakar ance masa Maishadan ko shadah.
No comments:
Post a Comment